27 Yuli 2019 - 06:26
Hormuz : Iran Ta Sallami Indiyawa 9

Iran ta sallami wasu ma’aikatan jirgin ruwa su 9, daga cikin 12, mambobin jirgin dakon man fetur na Panama (MT RIAH), data cafke a ranar 14 ga watan Yulin nan, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Indiya ta sanar a yau Juma’a.

(ABNA24.com) Saidai ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Indiya bata yi wani karin haske ba kan batun sakin ma’aikatan.

Gidan talabijin na PRESSTV, wanda ya nakalto labarin, ya ce, a yanzu ‘yan kasar Indiya 21 ne ake ci gaba da tsare da a Iran, da suka hada da uku na jirgin ruwan MT RIAH, da kuma wasu 18 na jirgin ruwan dakon man fetur na Birtaniya, Stena Impero, da dakarun juyin juya halin musulinci na Iran din suka cafke a makon da ya gabata a mashigar ruwan Hormuz.

Iran dai ta zargi jirgin ruwan MT riah, da dakon main a sumoga.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun- tsaka tsakanin gwamnatin ta Iran, da Birtaniya da kuma Amurka kan batun shige da ficen jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz.

Kafin hakan mahukuntan Iran, sun sanar da cewa a shirye suke suyi musayar jirgin ruwan na Birtaniya Stena Impero, kan jirgin ruwan Iran din Grace 1, da mahukuntan Gibraltar na Birtaniyar ke tsare da bisa zarginsa da sabawasafara man fetur zuwa kasar Siriya, dake karkashin takunkumin kasa da kasa.



/129